24 Satumba 2020 - 11:18
Zarif: Iran Da Rasha Suna Aiki Tare Domin Warware Matsalolin Wannan Yankin

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif, wanda ya isa birnin Moscow a jiya Laraba domin fara ziyarar aiki, ya fadawa manema labaru cewa; Babban jigon abinda zai tattauna da jami’an gwamnatin kasar Rasha a yayin ziyarar tasa da akwai yarjejeniyar Nukiliya.

ABNA24 : Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi ishara da matsayar Rasha tare da kasar Sin, a MDD danage kalubalantar yadda Amurkan take take dokokin kasa da kasa.

Muhammad Jawad Zarif ya kara da cewa; Da akwai aiki tare a tasakanin kasashen Iran da Rasha,da hakan ya bayar da damar tuntubar juna a tsakaninsu.

Wannan ita ce ziyara ta biyu da ministan harkokin wajen Iran din ya kai zuwa Rasha tun bayan bullar Corona.

342/